An haramta barar almajirai a Senegal
July 6, 2016Talla
Shugaba Macky Sall ya sanar da wannan mataki ne a lokacin wata hira da ya yi da manema labarai jim kadan bayan kammala Sallar idi karama da kasar ta sallata a wannan Laraba inda ya ce ya bai wa gwamnatinsa umarni kan ta dauki duk matakan da suka dace domin kawo karshen wannan tabi'ar ta ci da gumin yara marasa galihu da wasu mutane ke yi da sunan addinin Muslunci a kasar ta Senegal.
Wasu alkalumman bincike na gwamnatin kasar ta Senegal na shekara ta 2014 sun nunar da cewa almajirai kimanin dubu 30 ne akasarinsu 'yan asalin kasashe makobta ke yawon bara a birnin Dakar kadai a ko wace rana ta Allah sanye da tsumma kuma ba takalmi.