1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramta wa tshohon shugaban Brazil takara

Yusuf Bala Nayaya MNA
September 1, 2018

Kotun da ke lura da harkokin zabe a kasar Brazil ta haramta wa tsohon shugaban kasa Luiz Inacio Lula da Silva damar tsayawa takara duk da karin tagomashi na magoya baya da tsohon shugaban da ke tsare ke samu.

Brasilien Luiz Inacio Lula da Silva Ex-Präsident
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Peres

Wannan dai ya sanya kasar ta Brazil da ke zama babba a yankin Latin Amirka ta shiga rashin tabbas kan wanda ke zama fitaccen dan takarar shugabancinta a zaben watan Oktoba.

A zaman da alkalan kotun suka yi dai, shida ne cikin alkalan kotu bakwai ba su goyi bayan takarar ta Lula da Silva ba saboda tuhumar da ake masa da ta shafi cin hanci da rashawa har ta kai ga tsare shi kan tuhumar da tsohon shugaban ya ce ba ta da tushe.

Jam'iyyarsa ta Workers' Party ta sha alwashi na daukaka kara kan sakamakon hukuncin alkalan kotun zaben a Brazil, sai dai da dama na ganin daukaka karar ba lallai ta yi tasiri ba saboda shari'ar da ke gaban tsohon shugaban kafin zaben na Oktoba.