1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An hana 'yan adawa zanga zanga

Abdoulaye Mamane Amadou
March 19, 2021

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun haramta gangami da jerin gwanon da jam'iyyun adawa suka shirya don kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 21 ga watan Fabrairu.

Weltspiegel 24.02.2021 | Niger | Polizeieinsatz nach Wahlprotesten
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Cikin sanarwar da ya fitar, babban magajin garin Yamai yace ya dauki matakan hana zanga-zangar ne, saboda yiwuwar samun tada zaune tsaye a yayin gangamin, kana kuma da fargabar yaduwar annobar corona.

Jam'iyyun na adawa sun bayyana cewa za su ci gaba da jajircewa har sai an tabbatar da dan takarar jam'iyyun adawa Mahamane Ousmane a matsayin shi ne ya lashe zaben

Zanga-zanga dai ta barke jim kadan bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da Bazoum Mohamed a matsayin wanda yayi nasarar zaben na ranar 21 ga watan jiya, tare da sanadin mutuwar mutun biyu, baya ga wasu daruruwan mutanen da aka kama ciki har da tsohon madugun 'yan adawa Hama Amadou.