1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An harbe madugun adawar Yuganda a kafa

Binta Aliyu Zurmi
September 4, 2024

Jami'an 'yan sandar kasar Yuganda sun harbi madugun adawa kuma babban mai sukar lamirin gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni, Bobi Wine a kafa.

Uganda Kampala | Oppositionsführer Bobi Wine nach Angriff im Krankenhaus
Hoto: Abubaker Lubowa/REUTERS

Jam'iyyar Bobi Wine ta National Unity Platform ta ce harbin da aka yi wa shugabanta ya bar shi da mumunan rauni, amma yana samun kulawar likitoci a asibiti.

Arangama ce ta barke a yankin Bulinda da ke da nisan kilomita 12 da fadar mulki a Kampala, yayin da yake kan hanyarsa ta ziyarar lauyansa da kuma yake samun rakiyar magoya bayansa.

Sai dai yan sandan sun yi amfani da harsashen roba da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa su.

Magoya bayan Bobi Wine dai sun bayyana wannan harbi a matsayin wani mataki na kawar da dan adawar daga doron kasa wanda suka ce shugaba Museveni ne ke da alhaki.

A shekarar 2021 Bobi Wine ya tsaya takarar neman shúgabancin Yuganda, wanda ya garzaya kotu bisa rashin amincewa.