SiyasaArewacin Amurka
An harbe Kirk mai ra'ayin mazan jiya a Amurka
September 11, 2025
Talla
Maharin ya samu matashin da ke da kusanci da Shugaban Amurka Donald Trump a wuya, inda daga bisani hukumomi suka tabbatar da mutuwarsa a asibiti. A dai cafke mutum biyu da ake zargi da kai harin, amma daga bisani an sallame su bayan an gudanar da bincike kuma an tabbatar da cewa basu da hannu a kisan matashin mai shekaru 31.
Karin bayani:Trump ya sake tsallake rijiya da baya a yunkurin halaka shi
Shugaba Donald Trump ya nuna takaicinsa kan kisan gillar da aka yi wa Kirk, inda ya sha alwashin bin diddigin wadanda suka gudanar da aika-aikan da ya bayyana a matsayin 'mummunar rana a tarihin Amurka'. Kirk ya gabatar da jawabi a lokacin gangamin jam'iyyar Republican a wajen yakin neman zaben shugaba Donald Trump.