An harbe sojin Amirka A Jamus
March 3, 2011Talla
A tashar jiragen saman Frankfurt na ƙasar Jamus wasu sojin Amirka guda biyu sun mutu wasu kuma su biyu sun samu munanan raunuka bayan da wani ya harbe su. Dreban bus ɗin na sojin Amirka da wani takwaransa ne suka mutu cikin harbe-harben . An dai kame wani matashi mai shekaru 21 ɗan ƙasar Kosovo da ke zaune a birnin na Frankfurt . Ministan cikin gidan jihar Hessen, Boris Rhein ya ce ba a sani ba ko shin wannan hari na da nasaba ne da siyasa. Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce gwamnatin Jamus za ta yi iya ƙoƙarinta wajen gudanar da bincike akan wannan al'amari. Shugaba Barack Obama ya bayyana matukar alhininsa game da wannan hari.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu