1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An harbe sojojin NATO uku a Afghanistan

June 8, 2013

Rundunar dakarun tsaro ta NATO a Afghanistan ta ce wani sojan gwamnatin Afghanistan ya harbe wasu jami'anta guda uku da ke aikin bada horo a Paktika da ke arewacin kasar.

Der Nato-Stern und wehende Flaggen der Mitgliedsstaaten vor dem Gebäude des Nato-Hauptquartiers im belgischen Brüssel (Archivbild vom 5.9.1995)
Nato-Hauptquartier in BrüsselHoto: picture-alliance/dpa

A wata sanarwa da NATO ta fitar a wannan Asabar din ta ce mutumin da yi ya yi kisan na daga cikin wadanda jami'an na NATO ke bawa horo a kasar.

Kawo yanzu dai rundunar ba ta yi wani karin haske ba game da asalin kasashen da wadannan mutane da aka kashe su ka fito.

NATO dai ta kara da cewar za ta yi bayani ne bayan ta kammala tattaunawa da mahukuntan kasashen da jami'an da su ka riga mu gidan gaskiya su ka fito to sai dai rahotanni na cewar galibin jami'an na NATO da ke aiki a yanki da aka yi kisan Amurkawa ne.

Mwallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman