An harbo balan-balan leken asiri na Chaina
February 5, 2023Chaina ta nuna rashin jin dadi kan abinda ta kira amfani da karfi wajen kakkabo balan-balan din kasar da Amirka ta zarga da lekon asiri a wani bangare na sararin samaniyarta.
Wani jiragen yakin Amirka samfarin F-22 ne dai ya kakkabo balan-balan din da ya shafe tsawon kwanaki yana shawagi a sararin samaniyar Amirkar a daidai gabar tekun Carolin ta Kudu, bayan umarnin da mahukuntan Amirka suka bayar na daukar matakan da suka dace kan shawagin blan-blan din, kana a na cigaba da tattara ragowar baraguzan na'urar da Amirkar ta zargi Chaina da kokarin yi mata lekon asiri.
Wannan lamarin dai ya kara zafafa takaddamar diflomasiyyar da ta jima tana tsami a tsakanin kasashen biyu, wanda har ta kai ga babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, dage wata ziyarar kwanaki biyu da zai kai a Beijing.