1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An janye jirgin da ya rufe mashigar Suez

Abdul-raheem Hassan
March 29, 2021

Masar na asarar kudaden shiga da ya kai dala miliyan 12 zuwa 14 a duk rana tun bayan da jirgin ya toshe hanya, wanda ya yi sanadiyyar rike kayan kusan dala biliyan 10 tsakanin Turai da Asiya.

Ägypten Suezkanal Containerschiff Ever Given
Hoto: Mahmoud Khaled/Getty Images

Hukumomimn kasar Masar sun tabbatar da janye jirgin dakon kayan da ya toshe mashigar ruwan Suez kusan mako guda, matakin da ke sa fata mai kyau na budewar hanyar kasuwancin kasar nan ba da jimawa ba.

Mashigin ruwan na Suez, wanda ya hada Bahar Rum da tekun Maliya wato Red Sea, ya kasance kashin bayan harkokin sufurin teku na kasa da kasa tun bayan da amincewar jiragen ruwa su gudanar da zirga-zirga tsakanin kasashen Turai da kudancin Asiya ba tare da zagaye nahiyar Afirka ba.