An ji amon harbe-harbe a Khartoum
April 26, 2023Talla
To sai dai an ji amon harbe-harbe da shawagin jiragen yaki gami da tashin bama-bamai a birnin Khartoum a cewar jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Volker Perthes, a yayin wata gamnawa da ya yi da kwamitin tsaro na Majalisar.
Perthes ya bayyana cewar yana ci gaba da tattaunawa da bangarorin sojojin da ke fada da juna, a cewarsa babu wata alama da ke nuna suna da muradin hawa teburin tattaunawa.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, WHO ta yi gragadi a kan amfani da muggan sinadarai masu guba bayan da sojojin da ke fada da juna suka mamaye dakunan gwaje-gwajen kimiyya.
Ya zuwa yanzu, wannan rikici ya halaka rayukan mutane sama da 450 yayin da ya jikkata wasu dubbai.