1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An ji karar harbe-harbe a fadar shugaban Guinea Conakry

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 27, 2024

Sojojin da suka bude wutar wasu magoya bayan Kanar Celestin Bilivogui ne, wanda aka tsinci gawarsa ranar Laraba bayan kama shi da gwamnati ta yi

Hoto: Rebecca Blackwell/AP/picture alliance

An ji karar harbe-harben bindigogi a kusa da fadar shugaban kasar Guinea Conakry cikin daren Alhamis, inda kuma sojoji suka yi wa Conakry babban birnin kasar kawanya.

Karin bayani:Hukuncin daurin shekaru 20 wa Dadis Camara

Wani 'dan jarida mai suna Fode Toure da ke kusa da fadar shugaban kasar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa mutanen garin sun kidime bayan jin amon bindigogin, inda suka rinka guje-guje a dimauce, yayin da su kuma soji ke sintiri a kan tituna dauke da manyan makamai.

Karin bayani:Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya sauka a birnin Conakry na kasar Guinea

Wani jami'in gwamnatin kasar ya shaidawa AP cewa sojojin da suka bude wutar wasu magoya bayan Kanar Celestin Bilivogui ne, wanda aka tsinci gawarsa ranar Laraba bayan kama shi da gwamnati ta yi, kuma tuni aka harbe uku daga cikin sojojin masu bore.