1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An ji karar harbi a kusa da fadar shugaban Guinea Conakry

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 10, 2026

Tuni motocin silke na 'yan sanda da jami'an tsaro na musamman suka kafa shinge a kan hanyar zuwa kurkukun Conakry.

Shugaba Mamady Doumbouya na Guinea Conakry, yayin rantsuwar kama aiki a 2021 bayan juyin mulki
Shugaba Mamady Doumbouya na Guinea Conakry, yayin rantsuwar kama aiki a 2021 bayan juyin mulkiHoto: Cellou Binani/AFP

Karar harbe-harben bindiga ta karade kewayen babban gidan yarin kasar Guinea da ke yankin Kaloum na Conakry, babban birnin kasar, wanda kuma ke kusa da fadar shugaban kasa, kamar yadda shaidu suka tabbatar.

Wasu da ke makwabtaka da kurkukun sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa sun fara jin harbe-harben ne da karfe 9 na safiyar Talata, daga nan aka ci gaba da luguden wutar harsasai har tsawon sa'a guda.

Karin bayani : Kotu ta tabbatar da nasarar Doumbuya

Tuni motocin silke na 'yan sanda da jami'an tsaro na musamman suka kafa shinge a kan hanyar zuwa kurkukun, kuma zuwa wannan lokaci babu wani karin bayanin abin da ke faruwa daga mahukuntan kasar.