An ji tashin bama-bamai a birnin Yamai na Nijar
January 29, 2026
Mazauna birnin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa hayaki da haske ya turnuke sararin samaniyar birnin. Kazalika, wasu hotunan bidiyo da mazauna birnin suka wallafa a kafafen sadarwar intanet ya nuna yadda motocin sulke na sojoji ke sintiri a yankin.
Karin bayani:Nijar: Shekara guda bayan juyin mulkin soji
To amma rahotannin baya bayannan sun tabbatar da cewa al'amura sun lafa, kimanin awanni biyu da jin karar harbe-harben. Wani 'dan Nijar da ke goyon bayan gwamnatin soji, Ibrahim Bana, ya wallafa wani sako a shafinsa na Facebook, inda ya bukaci daukacin al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kare kasar daga duk wata barazana.
Karin bayani:Makomar Dimukuradiyya a kasashen da sojoji ke mulki
Babu rahotannin asarar rayuka sakamakon farmakin na birnin Yamai, da ke zama barazana ga gwamnatin Janar Abdourahamane Tiani, wanda ya hau kan karagar mulki shekaru biyu da suka gabata bayan hambarar da gwamnatin dimukuradiyya.