An jikata 'yan aikin agaji a Siriya
February 8, 2014Kafofin yada labarai na gwamnatin kasar Siriya sun ruwaito cewa an jikata ma'aikatan agaji hudu na kungiyar Red Crescent, lokacin da suke aikin jinkai cikin yankin Homs wanda ke hannu 'yan tawaye.
Sanarwar ta ce an bude wuta kan tawagar 'yan agajin. Ana ci gaba da samun tarnakin kai kayan agaji saboda yadda duk bangarorin ke zargi juna da saba yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla. Shugaba Bashar al-Assad na kasar ta Siriya da bangaren 'yan tawaye sun amince da wata tudun dafawa a karon farko yayin taron birnin Geneva, amma yanzu wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta tana neman zama shiririta.
Masu fafutuka sun ce gwamnati ta cilla kimanin rokoki 11 cikin yankin da ke hannun 'yan tawayen.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal