1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An jinjina wa sojojin Nijar bayan nasara a kan 'yan ta'adda

Gazali Abdou Tasawa MA
October 22, 2021

'Yan Nijar sun yi farin cikin da jinjina ga sojojin kasar a game da halaka 'yan ta'adda a wata arangama da ta hada su a wani kauyen yankin Banibangou na jihar Tillabery.

Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Sojojin sun rutsa da ‚yan ta'adda ne jim kadan bayan wani hari da suka kai a kasuwar wani kauye inda suka halaka mutane hudu tare da kwashe dabbobi.Wakilinmu a Yamai Gazali Abdou tasawa na dauke da karin bayani a wannan rahoto da ya aiko mana.

Bayanai daga yankin na gundumar Banibangou na jihar ta Tillabery, sun bayyana cewa da yammacin ranar Alhamis ne ‘yan ta’adda dauke da manyan bindigogi bisa baburra kimanin 40 suka kai hari a kasuwar kauyen Mial Hamani da da ke a nisan kilomita 35 da karamar hukumar Abala inda suka kashe mutane hudu suka kona motoci da kayan abinci tare da yin awon gaba da tarin dabbobin jama’ar kauyen.

Bayan dauki ba dadi na wani lokaci, sojojin gwamnatin kasar ta Nijar sun yi nasarar halaka ilahirin maharan su kimanin 40. Kuma Dr bunty Diallo mai sharhi kan harkokin tsaro a jamhuriyar ta Nijar ya fassara wannan nasara da sojojin Nijar suka samu da tasirin da bayar da bayanai ya yi a cikin lamarin.

Ita ko kungiyar Action For Humanity wacce ke gudanar da ayyukan jin kai a yankin ta bakin Magatakardanta Malam ibrahim Dambaji, ta ce aiki da gwamnati ta fara yi da shawarwarin al’uma da kuma samun hadin kan al’umma ga sojoji, ya taimaka ga cimma wannan nasara.

Wannan nasara da sojojin Nijar suka samu kan ‘yan ta’adda a yankin na Shinegoder na zuwa ne kwana daya bayan kisan da ‘yan ta’addan suka yi wa sojojin Nijar 11 a harin da suka kai wa ayarin motocin shugaban gundumar Bankilare a ranar Larabar da ta gabata.

A ranar Larabar kawancen sojojin Nijar da na Burkina Faso da kuma na Chadi, ya yi nasarar halaka gwamman ‘yan ta’adda a yankin magangamar iyakoki uku na Nijar da Mali da Burkina Faso tare da karbe tarin makamai da harsasai da kuma lalata babura masu yawa.