An kaddamar da aikin yaki da kyandar Biri a Kwango
October 6, 2024Talla
Cutar da hukumar lafiya ta Majalaisar Dinkin Duniya ta bayyana ta da cewa cuta ce da ke neman daukin gaggawa yanzu a duniya, ta kuma bazu zuwa wasu yankuna na duniya daga Kwangon.
Alluran rigakafi dubu 265 da Tarayyar Turai da Amurka suka bai wa Kwangon, tuni aka fara yi wa mutane a birnin Goma da ke arewacin lardin kivu a ranar Asabar.
Yanki ne da dama ke fama da barnar cutar, musamman sabon nau'inta mai saurin yaduwa.
Ya zuwa yanzu dai Kyandar ta Biri ta kashe mutane 859, daga cikin kimanin mutane dubu 30 da suka kamu da ita a kasar.
Karin Bayani:An samar da makuden kudi na dakile cutar Mpox a Afirka