An kaddamar da hare-haren kan mayakan IS a Siriya da Iraki
April 5, 2015Talla
Hare-haren da suka kaddamar dasu cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an kai guda 12 ne a sansanonin mayakan IS din ne da ke a Masoul na kasar Iraki.
Sabbin hare-haren na zuwa ne yayin da ake kwashe mutane 2000 akasari, falasdinawa, daga sansanin ‘yan hijira na Yarmuk dake Damascus na kasar Syria, bayan karbe kusan ilahirin yankin da mayakan IS suka yi.
Kamar yadda wani jami'an wata kungiyar Falasdinawa, Anwar Abdul Hadi ya fada a yau, an kwashi mutanen 2000 ne tsakanin ranar Juma'a da jiya Asabar, inda aka bi dasu ta wasu hanyoyin da ke da tsaron sojin da suka hana mayakan na IS wuce yankin dake cikin lardin Zahira.