An kaddamar da sabbin ministocin Japan
December 26, 2012Talla
Sabon Firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya kaddamar da sabuwar majalisar gudanarwa, wadda ke da alhakin kawo ci gaba ga tattalin arzikin kasar.
Abe ya bayyana sunayen sabbin ministocin jim kadan bayan majalisar wakilai da ta dattawa sun zabe shi kan mukamun na firamnistan, sakamakon rinjayen da jam'iyyarsa da LDP ta samu yayin zaben 'yan majalisu a farkon wannan wata na Disamba.
An zabi tsohon firaminista Taro Aso a matsayin ministan kudi kuma mataimakin firaminista.
Shinzo Abe ya zama firaministan kasar ta Japan na bakwai cikin shekaru shida, kuma yanzu yana da aiki samar da ci gaban tattalin arziki ga kasar wadda ke zama na uku wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu