An kafa dokar hana yawo a Kamaru
October 1, 2018
Talla
Hukumomi sun kafa dokar hana yawo na sa'o'i 48 daga wannan Litinin a yankin, musamman a yankunan da suka fuskanci tashin hankalin da ya kai ga asarar rayuka.
Lamarin na zuwa ne mako guda da babban zaben kasar.
Rahotanni sun ce an yi ta jin karar harbe-harbe cikin daren Lahadin da ya gabata a garin Buea, yankin da ke zama cibiyar rigimar.
Shaidu sun ce dukkanin manya da kananan shagunan hada-hada sun kasance a rufe yayin da ita ma zirga-zirgar ababen hawa ta tsaya cik.
Akalla rayuka 40 ne 'yan sanda suka halaka a ranar daya ga watan Oktobar bara a yankin, lokacin da masu da'awar kafa kasar Ambazoniya suka yi bore.