An kafa dokar ta baci a Turkiya
July 21, 2016Talla
Gwamnatin ta yanke wannan shawara ce a karshen wani taron koli na hukumomin tsaro da na majalisar ministoci a birnin Ankara. Dokar ta bacin za ta ba da damar kaddamar da dokar hana fita da takaita izinin yin taruka da kuma yin zirga-zirga a wasu wuraran da aka tantance, ba tare da shugaban ya bi ta hanyar majalisar dokoki ba.
Yanzu haka tun bayan yunkurin juyin mulkin mutane kusan dubu 55 aka kama daga malaman makaranta da 'yan sanda da alkalai da sojoji, ake tsare da su wadanda ake zargi da hannu a lamarin.