1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa rundunar kariyar agaji a Somaliya

August 14, 2011

Duk da cewa ƙungiyar Alshabaab ta fice daga birnin Mogadishu, amma har yanzu akwai barazanar tsaro. wannan ya haifar da kafa rundunar soji ta musamman domin rakiyar kayan agajin.

Ma'aikacin taimakon agaji a SomaliyaHoto: dapd

Gwamnatin Somaliya ta kafa wata rundunar sojin da za ta riƙa rakiyar masu raba kayan agajin gaggawa, da kuma lura da sansanonin da ake kafawa domin ajiyar kayan abinci. Gwamnatin ƙasar ta ce kafa rundunar ya zama wajibi, a dai dai lokacin da tamowa ke hallaka jama'a, amma rashin tsaro ya hana ƙasashen duniya kai agaji.

Sansanin yan gudun hijira a SomaliyaHoto: dapd

Duk da cewa ƙungiyar Alshabaab ta fice daga birnin Mogadishu, amma har yanzu akwai barazanar kai harin ƙunar bakin wake da kuma na sari ka noƙe. Yanzu haka dai a karon farko jirgin dake dauke da abinci ya sauka a ƙasar ta Somaliya, yayinda ake ta jigilar wasu abincin da aka tara daga ƙasar Kenya. Dakarun kiyayen zaman lafiya na Tarayyar Afirka dai sune ke bada tallafin tabbatar da tsaro a ƙasar Somaliya wanda yaƙi ya dai-ɗaita. Inda Uganda ta ce za ta tura ƙarin soji 2000 a Somaliya.

Mawallafi : Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tanko Bala