SiyasaAfirka
Hari a Jamhuriyar Benin
June 6, 2025
Talla
Rahotanni da kasar Jamhuriyar Benin sun nuna cewa wani harin mayakan masu ikirarin jihadi ya halaka sojoji uku da 'yan sanda biyu a yankin arewa masu yammacin kasar. Majiyoyin tsaro sun ce an kai hari a ofishin 'yan sanda na Tanougou.
Karin Bayani: Mayakan jihadi sun kashe sojojin Benin 70
Ita dai Jamhuriyar Benin tana fuskantar tashe-tashen hankula na kungiyoyin Jihadi a iyakar kasarda kasashen Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar.
Kasashe uku na Mali da Burkina Faso gami da Jamhuriyar Nijar suna fuskantar hare-hare tsageru masu ikirin jihadi, inda sojoji suka yi juyin mulki a duk kasashen uku, sannan kasashen uku suka fice daga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS.