An kai hari a wani gidan shakatawa a Kenya
October 24, 2011Mutane 12 suka jikkata bayan da wani gurnati ya tashi a wani gidan shakatawa da ke tsakiyar Nairobi babban birnin Kenya. Wani gidan radio a babban birnin mai suna Capital Radio ya rawaito wasu shaidu wadanda suka ce wani mutumi wanda ya nemi da a bar shi ya shiga gidan da misalin karfe ukku na dare, ya jefa gurnetin a gidan ya kuma ranci na kare.
Wannan hari dai na zuwa kwanaki biyu bayan da ofishin jakadancin amurka a Kenya ya yi gargadin afkuwan hari a Nairobi.
Hukumomi a Nairobi suna dora alhakin harin a kan kungiyar Al-Shababa wacce ake zargi da satan baki daga kasar Kenyan wacce kuma ke barazanar yin kafar ungulu ga arzikin da kasar ta ke samu daga sashinta na kula da shakatawa da yawon bude idanu. Dakarun Kenya sun kori 'ya'yan kungiyar ta Alshabab zuwa Somaliya, kuma kungiyar ta yi barazanar kai hare-hare idan har dakarun na Kenya basu daina fatattakarsu ba. Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin wannan hari
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita : Halima Balaraba Abbas