1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kai hari filin jiragen sama na Khartoum

October 21, 2025

Mazauna Khartoum na Sudan na cikin fargaba sakamakon hare-haren jirage marasa matuka a filin jirgin saman birnin.

Filin jirgin saman Khartoum Sudan
Filin jirgin saman Khartoum Sudan Hoto: AFP

Harin na zuwa a daidai lokacin da ake kokarin sake bude filin jiragen saman domin ci gaba da gudanar da zirga-zirgar cikin gida tun bayan shekaru biyu da rufe shi, sakamakon yakin da ake gwabazawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar kar-ta-kwana ta RSF.

Karin bayani: Mayakan RSF sun kai hari Port Sudan

Shaidun gani da ido sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sun ji karar tashin bama-bamai sakamakon hare-haren jirage marasa matuka a yankin tsakiya da kuma kudancin birnin Khartoum da ke daura da filin jirgin babban birnin.