An kai hari kan ofishin jakadancin Masar da Daular Larabawa a Tripoli
November 13, 2014Talla
Wasu hare-haren bam da mota da aka kai a wajen ofishin jakadancin Kasashen Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa a Tripoli babban birnin kasar Libiya sun lalata gine-ginen. Jami'ai sun ce ba wanda ya samu rauni sakamakon tagwayen hare-haren da ya auku a wata unguwa da ke kunshe da ofisoshin jakadu kasashen waje da ke a babban birnin na Libiya. Tuni dai Masar ta yi Allah wadai da harin tana mai cewa ya yi mummunar illa ga dadaddiyar dangantaka ta jini tsakaninta da Libiya. A cikin wata sanarwa ma'aikatar harkokin wajen Masar ta ce kungiyoyin 'yan ta'adda na amfani da tarzoma don cimma manufofi na siyasa. Libiya ta tsunduma cikin tashe-tashen hankula tun bayan kashe shugaban mulkin kama karya Muammar Gaddafi a shekarar 2011.