1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan sojojin Yemen

Abdul-raheem Hassan
December 29, 2019

Akalla sojoji shida sun mutu da wasu kananan yara uku a wani harin makami mai lin zami da aka harba a farfajiyar faretin yaye sojoji a al-Dhalea.

Jemen Anschlag auf Polizeikräfte in Aden
Hoto: Reuters/F. Salman

Wasu hotunan harin da ke yawo a yanar gizo ya nuna gawarwakin mutane da dama a kwance, sama da mutane 20 sun jikkata.

Dakarun kasar Yemen na zargin mayakan Houthi da kai harin, sai dai 'yan tawayen ba su ce komai ba.

An fara yakin kasar Yemen a 2014 bayan da 'yan Houthi suka nuna sha'awar kwace iko da babban birnin aksar Sana'a, suka tilastawa Shugaba Abed Rabbo

Mansour Hadi yin hijira.