An kai harin roka a Kenya
October 27, 2011A ƙasar Kenya 'yan sanda a sukace an harba roka kan wata mota dake ɗauke da ma'aikatan gwamnati, inda mutane hudu suka mutu. Wata motar dake ɗauke da jami'an tsaro da ma'aikatan ilimi ne aka kaiwa farmaki a yakin da iyakar ƙasashen Kenya da Somaliya, ka wo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin harin. Kakakin 'yan sanda Kenya Erik Kiraithe ya tabbatar da harin, amma ba yi ƙarin haske ba. Wannan harin dai yazo ne kwanaki uku bayan harin gurneti har sau biyu da aka kai a birnin Nairobin Kenya. Jami'an tsaron Kenya na zargin tsagerun ƙungiyar Al-Shabab da hannu a hare-haren. Bisa barazanar da ƙungiyar ta yi na ɗaukar fansa bisa kutsen da sojojin Kenya suka yi cikin ƙasart Somaliya don farauto waɗanda ke sace baƙi cikin ƙasar ta.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu