An kai sabbin hare-hare a kudancin Afghanistan
December 8, 2007Talla
Dakarun sojin Afghanistan bisa jagorancin sojin tsaro na Nato, sun ƙaddamar da wasu sabbin hare-hare a kudancin ƙasar. Matakin ya zo ne a ƙoƙarin ƙwato garin Musa Qala ne, dake hannun tsagerun ƙungiyyar Taliban. A yanzu haka dai an shafe kusan watanni goma ke nan garin na Musa Qala na hannun tsagerun na Taliban. Ana zargin cewa tsagerun na amfani da garin ne, a matsayin cibiyar hada-hadar muggan ƙwayoyi. Yankin dai na Helmand dake kusa da garin Musa Qala, yankine da ya yi ƙaurin suna wajen shuka muggan kwayoyi da kuma hada-hadarsu.