Tsohon shugaban Sudan yana gidan fursuna
April 17, 2019Tsohon Shugaba Omar al-Bashir na Sudan dan shekaru 75 da haihuwa da masu zanga-zanga suka kawo karshen mulkinsa yana wani gidan fursuna da ake kira Kobar da ke Khartoum fadar gwamnatin kasar, bayan an fitar da shi daga fadar shugaban kasa, kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta tabbatar.
A wani labarin wani jagoran 'yan tawaye su Sudan a jihohin Blue Nile da Kudancin Kordofan ya bayyana tsagaita wuta ta radin kai tsakanin 'yan tawayen da sojojin gwamnati na tsawon watanni uku. A cikin wata sanarwar Abdulaziz al-Hilu shugaban kungiyar 'yan twayen SPLM-N ya ce matakin nada nasaba da sauye-sauyen siyasa da aka samu a kasar domin ganin matakan da sabbin mahukun Sudan za su dauko domin dakile tashe-tashen hankula da ake samu a wasu sassan kasar gami da mayar da mulki hannun farar hula cikin kwanciyar hankali.
Masu zanga-zanga a Sudan sun kawo karshen gwamnatin ta al-Bashar ta shekaru 30 bayan shafe makonni a helkwatar tsaro ta kasar.