An kai wa Boko Haram Farmaki a Kano
September 17, 2012Jami'an tsaro a Tarayyar Najeriya sun yi ikirarin hallaka kakakin kungiyar Kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnati Lidda'awati Wal Jihad wacce aka sani da
Boko Haram bayan wani samame da suka kai maboyar su.
Jami'an tsaron sun bayyana cewa sun samu nasarar kame wasu shugabannin kungiyar nan mai gwagwarmaya da makamai don kafa shari'ar musulunci a Tarayyar Najeriya da aka fi sani da Boko Haram guda uku inda daya daga cikin su ya mutu a asibiti wanda suke zaton cewa kakakin Kungiyar wanda ake kira da Abul Qaqa.Rundunar hadin gwiwa mai aikin wanzar da zaman lafiya da ake kira JTF a Kano ne suka kai wannan hari kan manyan shugabannin kungiyar gwagwarmayar sai dai tana bincike don tabbatar da cewa kakakin kungiyar ne ta hallaka.
Duk da dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labari, amma dai wata kafa ta jami'an tsaron ta hakikance cewa sun kashe Abul Qaqa wanda shine mai mu'amala da kafafen yada labarai don fayyace matsayin kungiyar. Ko yaya ‘Yan Najeriya musamman mazauna yankin Arewa maso gabashin Najeriya suka ji da wannan labari ganin ana fafutukar nemo bakin zaren warware tashin hankali da hare-haren da ‘yan kungiyar ke kaiwa. Mumammad Abba Sani wani mazaunin Maiduguri ne da tashe-tashen hankulan gari ya tilasta shi kaura daga zuwa nan Gombe.
"A baya ma dai Jami'an tsaron sun bayyana cewa sun kame gami da hallaka kakakin kungiyar ta Ahlis Sunnati Lidda'awati Wal Jihad a Kaduna labarain da kungiyar ta fito karara ta karyata".
Wannan yasa talakawan kasar bayyana shakku kan sahihancin wannan labari kamar yadda Hamza Auwal Hamza ya bayyana. Har ya zuwa lokacin da na kamala hada wannan rahoto Jama'atu Ahlis Sunnati Lidda'awati Wal Jihad wacce aka sani da Boko Haram ba ta ce komai kan wannan labari ba.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnonin yankin Arewacin Najeriya su ka kamalla shiri na shigar da gwamnatin Tarayyar Najeriya da shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan ƙara a kotu, saboda rashin bada kudade na magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin. Gwamnonin dai sun bayyana cewa suna kashe kudaden da ya kamata su yi wa talakawa aiki wajen sayen motoci da sauran kayyakin aiki ga jami'an tsaro kuma gwamnatin Tarayyar bata tallafa musu, inda tafi maida hankali a Abuja fadar gwamnatin Tarayya.
Mawallafi: Amin Sulaiman Muhammed
Edita: Usman Shehu Usman