An kai wa Japan harin ta'addanci
July 18, 2019Talla
Wani baban jamai'in 'yan sanda na yankin, ya ce wani mutum ne ya afka wa masana'antar inda bai yi wata-wata ba ya cinna mata wuta, ya kara da cewa, wannan shi ne karon farko da Japan ke rasa rayuka mai yawan gaske a lokaci guda a sanadiyar harin da tuni ake zargin na ta'addanci ne.
Wadanda suka sami raunin na cikin mawuyacin hali, abin da ya sa ake fargabar alkaluman mamatan ka iya haurawa. Shugaban masana'antar ya ce, daman sun jima suna fuskantar barazana daga wurin wasu da ba asan ko su waye ba, da ke aiko musu sakonnin email akai akai.