Nijar: Mutum 10 sun mutu a harin 'yan bindiga
March 25, 2021
Yanzu haka an tabbatar da mutuwar mutum akalla goma a wani sabon hari da ake zargin 'yan bindiga da kai wa, a wasu kauyuka da ke a yankin Tillaberi. Wani babban jami'in tsaron kasar, ya ce, maharan a yayin kai harin, sun kona wata makaranta da ke a kauyen Zibane inda a aka rasa rayuka uku sauran bakwai kuma a kauyen Gabado aka halaka su, ya baiyana fargabar karuwar alkaluman mamata a sakamakon harin na jiya Laraba.
Kawo yanzu dai, ba a kai da gano wadanda keda hannu a harin da ke zuwa bayan wani munmunan harin da ya halaka mutum kimanin dari da talatin da bakwai a ranar Lahadin da ta gabata a yankin kudu maso yammancin jamhuriyyar ta Nijar ba. Hare-haren masu nasaba da aiyukan 'yan ta'adda, na zuwa ne a daidai lokacin da aka bude taron kasa da kasa kan batun inganta tsaro a kasashen yankin Sahel da na Tafkin Chadi, a Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar.