1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama dubban masu bore a Faransa

October 19, 2026

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ta rikide zuwa tarzoma a Paris da wasu biranen kasar.

Zanga-zangar tsadar rayuwa a Faransa
Zanga-zangar tsadar rayuwa a FaransaHoto: Sylvain Thomas/AFP

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Faransa ta ce an kama kusan mutum 2,400 a ranar Asabar, yayin da jami'an 'yan sanda kimanin 1,000 suka jikkata, bakwai daga cikinsu kuma suka samu munanan raunuka.

Shugaba Macron ya ce gwamnatocin kananan hukumomi ka iya haramta gudanar da zanga-zangar idan bukatar hakan ta taso, sai dai bai ayyana dokar ta-baci ko sanya dokar hana fita ba. Zanga-zangar ta hada da kungiyoyin kwadago da dalibai da ke nuna fushinsu kan tsadar rayuwa da karancin damar samun kyakkyawar makoma ga matasa.

Karin bayani: Zanga-zangar tsadar rayuwa ta zama tashin hankali a Faransa da Beljiyam

An kuma wawashe shagunan jam'a tare da kona gine-ginen gwamnati yayin tarzomar. Kazalika 'yan adawa na ci gaba da sukar yadda Macron ke tafiyar da rikicin, watanni kadan kafin zaben shugaban kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW