1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An kama fasinjan da ya yi yunkurin bude kofar jirgin sama

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 12, 2025

Kamfanin jirgin saman Cathay Pacific ya ce a yayin faruwar balahirar, babu wani fasinja ko ma'aikacinsa da ya samu rauni

Filin jirgin saman Hong Kong a shekarar 1998
Hoto: Frederic J. Brown/epa/AFP/picture-alliance

'Yan sandan Hong Kong sun cafke wani fasinja bisa laifin yunkurin bude kofar jirgin sama, lokacin da yake tsaka da tafiya a sararin samaniya, bayan taso wa daga birnin Boston na kasar Amurka, a kan hanyar zuwa Hong Kong din.

Kamfanin jirgin mai suna Cathay Pacific, ya ce a yayin faruwar balahirar, babu wani fasinja ko ma'aikacinsa da ya samu rauni, kuma jirgin ya sauka lafiya ranar Alhamis.

Karin bayani:Mutane 83 sun mutu a gobarar Hong Kong

Tuni 'yan sandan suka kaddamar da bincike bayan kama matashin da ake zargi da wannan katobara, mai shekaru 20 'dan asalin kasar China.