1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamen Jamusawa saboda kin baki

Yusuf Bala Nayaya
October 1, 2018

Mai gabatar da kara a birnin Karlsruhe na Jamus, ya nunar da cewa muntane shida ne masu kyamar baki a birnin Chemnitz na gabashin kasar aka kama, bisa zargin hada wata kungiya ta 'yan ta'adda.

Chemnitz Deutschland Rechtsextremismus Neo-Nazis
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Meyer

Wata majiya ta jami'an tsaro ta fada wa kamfanin dillancin labaran Jamus na dpa cewa daya daga cikin mutanen shida an kama shi ne a kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki a jihar Bavaria da ke kudancin kasar ta Jamus.

Kisan wani Bajamushe da ake zargin wasu baki da aikatawa ne dai ya janwo zanga-zangar adawa da bakin a birnin na Chemnitz. Mutanen shida da aka kama an kama su ne bayan wani samamen 'yan sanda da nufin kama wadanda ake zargin cewa suke da alhaki wajen hada wata kungiya mai tsananin kin jinin baki mai suna Revolution Chemnitz.