Ghana: Cafke mai yunkurin juyin mulki
February 12, 2022An kama Oliver Barker-Vormawor shugaban kungiyar masu matsa lamba ta #FixTheCountry wanda ya jagoranci zanga-zanga a kasar Ghana da ke yammacin Afirka kan matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da kasar ke ciki, a filin jiragen sama a ranar 11 ga watan nan na Febrairun da muke ciki lokacin da ya dawo daga Birtaniya.
Barker-Vormawor ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, zai yi juyin mulki idan majalisar dokokin kasar Ghana ta amince da wani kudiri mai cike da cece-kuce wanda aka fi sani da E-Levy. Kudirin yana gabatar da harajin kaso 1.75 cikin 100 kan hada-hadar kayan lantarki da suka hadar da biyan kudin wayar hannu.
Ana sa ran gurfanar da matashin a gaban kuliya, a ranar Litinin 14 ga wannan wata na Febrairu. Dama dai kasar Ghana ce abin kwatance a yammacin Afirka wajen kwatanta dimukuradiyya mai dorewa, duk da cewa zabukan 2021 na fuskantar zargi daga bangaren 'yan adawa kan magudin zabe da kuma mutuwar mutane a rikicin zabe.