1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama masu buga kudin jabu a Spaniya

March 3, 2024

Jami'an 'yan sanda a kasashen Spaniya da Italiya da kuma Girka sun kai farmaki kan wata kungiyar miyagu 'yan asalin Pakistan da ke bugawa da kuma rarraba jabun kudade.

An kama masu buga kudin jabu a Spaniya
An kama masu buga kudin jabu a SpaniyaHoto: Napoli/Giacomino/ROPI/picture alliance

'Yan sanda sun ce miyagun sun samar da kudaden bogin da ya suka kai kimanin euro miliyan daya a takadar kudi ta euro dari-dari. Rundunar 'yan sandan Spaniya ta ce, za a iya rarraba jabun kudaden a injinan ATM ba tare da an sani ba.

Tuni dai jami'an suka ce sun kama mutum 14 daga biranen Barcelona da kuma Rome ciki har da shugaban kungiyar.

Tun a watan Nuwamban bara ce dai 'yan sanda suka baza komarsu bayan da aka gano jabun kudade na yawo a birnin Barcelona.