An tsare masu gwanjon mata a internet
January 4, 2022Talla
'Yan sanda a kasar Indiya sun kama wasu matasa biyu mace da miji, wandan da ake zargi da hannu a samar da manhajar boge inda ke gwanjon hotunan fitattun mata musulmai.
A makon jiya ne hotunan wasu fitattun mata musulmi 'yan Indiya fiye da 100 suka cike manhajar "Bulli Bai" ba tare da izinin su ba, ciki har da 'yan jarida da masu fafutuka da taurarin fina-finai da masu fasaha har da mahaifiyar wata daliba 'yar Indiya da ta bace mai shekaru 65 da Malala Yousafzai wacce ta lashe kyautar Nobel.
Tuni dai hukumomi suka soke manhajar da ake gwanjon hotunan duk da cewa an riga an wallafa hotunan su da dama, amma ba a cimma wani ciniki ba.