1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

An kama ma'aikatan kamfanin hakar zinare a Mali

Suleiman Babayo AH
November 26, 2024

An kama ma'aikatan kamfanin hakar zinare mallakin kasar Kanada da suke aiki a kasar Mali.

Mali I Assimi Goita shugaban gwamnatin mulkin soja
Assimi Goita shugaban gwamnatin mulkin sojan MaliHoto: Fatoma Coulibaly/REUTERS

Wani kamfanin kasar Kanada da yake aikin hakar zinare a kasar Mali ya ce an kama ma'aikatansa hudu a wannan Talata, yayin da gwamnatin mulkin sojan kasar take neman karin kudi daga kamfanonin hakar ma'adanai da suke aiki a kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Karin Bayani: Zargin take hakkin dan Adam a Mali

Tuni wasu majiyoyi da ke kasar suka tabbatar da kama ma'aikatan hudu na kamfanin Barrick Gold mallakin kasar Kanada, kuma wadanda aka kama manyan ma'aikatan kamfanin 'yan kasar ta Mali.Ita dai kasar Mali tana sahun gaba na kasashen Afirka masu arzikin zinare. Babban jami'in kamfanin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa suna fatan warware sarkakiyar da gwamnatin mulkin sojan kafin karshen wannan shekara ta 2024 da muke ciki.