An kama masu niyar gudanar da ayyukan tarzoma a Jamus
October 2, 2011Talla
Jami´an tsaron a nan birnin Bonn na Tarayya Jamus sun cafke wasu mutane guda ukku masu tsatsauran ra´ayin addinin musulunci bisa zargin shirya makarkashiyar kai harin ta´adanci a daidai lokacin da birnin ke shagulgulan cikar shekaru 21 da sake hadewar kasar. Kana a kusa da birnin Frankfurt da ke tsakiyar jamus ma an cafke mutum guda bisa zargin kitsa manakisar harin ta'addanci.
kakakin rundunar 'yan sandar Jamus yace an samu mutanen hudu da wasu sinadarai na hada bam-bamai. Ranar litinin nan ne dai,a fadin tarayyar Jamus baki daya ,ake bikin cika shekaru 21 da samun hadin kai tsakanin Jamus ta gabas da ta yamma. A shekara bana dai birnin Bonn aka dorawa yaunin karbar bikin na kasa baki daya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman