An kama mutumin da ya jikkata mutane da mota a Stuttgart
May 2, 2025
Talla
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane da dama sun ji mumunan rauni, bayan da mutumin ya hau kansu da motar alfarma kirar Mercedez G-Class SUV a tsakiyar birnin Stuttgart.
Karin bayani: Dan Siriya ya markade motoci a Jamus
Rundunar ‘yan sandan birnin ta bayyana a shafinta na sada zumunta cewa lamarin ya faru ne a wani yanki mai dandazon jama'a wanda ke kusa da sansanin jami'an tsaro.
Karin bayani: Mutun 5 sun mutu a harin kasuwar Kirisimeti a Jamus
Ya zuwa yanzu dai 'yan sanda ba su yi karin haske kan ko lamarin na da alaka da hari ko makamancin haka ba, sai dai an tsare direban motar nan take. A baya-bayan an sha samun hare-haren da mota kan jama'a a wasu sassan kasar.