SiyasaArewacin Amurka
An cafke Ismael El Mayo Zambada
July 26, 2024Talla
Ma'aikatar shari'a a Washington ta ce an kame dilalan miyagun kwayoyin, Ismael El Mayo Zambada, da dan tsohon abokin aikinsa Joaquin El Chapo a Texas. Mutanen biyu yan kasar mexiko na fuskantar tuhume-tuhume da yawa a Amurka, saboda jagorantar ayyukan ta'addanci, ciki har da masana'antar Fentanyl mai safarar hodar ibilis da kuma safarar mutane, Zambada shi ne wanda ya kafa sanannar kungiyar 'yan dabaR nan, ta Sinaloa Cartel tare da El Chapo Guzman,wanda aka mika shi zuwa Amurka a shekara ta 2017 inda aka yanke masa hukuncin daurin rai-da rai.