1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kama tsohon minista a Jamhuriyar Nijar

January 6, 2024

Hukumomi a Nijar sun cafke wani tsohon jigon rusasshiyar gwamnatin kasar, wanda ke cikin jerin wadanda sojoji ke nama ruwa-a-jallo. babu dai bayanai a kan laifin da ya aikata

Tsohon Minista a Nijar, Ibrahim Yacoubou
Tsohon Minista a Nijar, Ibrahim YacoubouHoto: DW/N. Amadou

An kama tsohon ministan makamashi na Jamhuriyar Nijar, Ibrahim Yacouba, wanda ya yi aiki a zamanin gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka hambare cikin watan Yulin bara.

Shi dai Ibrahim Yacouba, ya tsere daga Nijar din ne jim kadan bayan kwace iko da sojojin suka yi, kuma an kama shi ne lokacin da ya sauka filin jirgin sama na birnin Yamai.

Tuni ma dai wata majiyar ta nuna cewa an ma tsare shi ba kuma tare da an sanar da laifin da ya aikata ba.

Ibrahim Yacouban na daga cikin fitattun jami'ai 20 da gwamnatin sojin Nijar din ta bayyana neman su ruwa-a-jallo cikin watan Satumba.

Tsohon ministan na Nijar dai ya koma kasar ne a jiya Juma'a, daga wata kasa ta yankin Maghreb.