1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kama wadanda ke da hannu a yunkurin juyin mulki a Saliyo

November 27, 2023

An kama galibin wadanda ke da hannu a yunkurin juyin mulki a Saliyo

Hoto: Cooper Inveen/REUTERS

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, ya ce wadanda suka jagoranci kai harin, sun kaddamar da farmaki kan barikokin  sojoji da gidajen yarin kasar, kafin daga bisani dakarun gwamnati suka murkushe su.

Karin bayani :

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna daruruwan fursunonin a kan tituna, a yayin da ake ta jin karar harbe-harbe tsakanin dakarun sojin kasar da maharan a babban birnin kasar Freetown.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da al'amuran siyasa da dimukradiyya ke gamuwa da cikas a kasashen yammaci da tsakiyar Afrika, ta hanyar juyin mulki. Daga shekara ta 2020 kawo yanzu akalla an yi juyin mulki sau 8, ciki har da jamhuriyar Nijar da Gabon a wannan shekara ta 2023.

Karin bayani: Ana boren adawa da tsadar rayuwa a Saliyo

Tuni dai kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta ce wannan hari wani yunkuri ne na tada-zaune tsaye tare da mallakar muggan makamai da kuma haifar da tazgaro ga kundin tsarin mulkin kasar.