An kama wanda su ka kai harin bam a Isra'ila
November 23, 2012Daga cikin wanda aka kama ɗin kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan ƙasar Micky Rosenfeld ya shaidawa manema labari, akwai balarabe ɗaya wanda ɗan asalin ƙasar ta Isra'ila ce da kuma wasu falasɗinawa da kakakin ya ce su na da alaƙa da Hamas da kuma 'yan ƙungiyar nan ta Islamic Jihad to sai dai kawo yanzu hukumomin ƙasar ta bani yahudu ba su fayyace sunayen wanda aka kaman ba to sai dai sun ce su na nan su na faɗaɗa bincike ko ya Allah za a samu ƙarin wanda ke da hannu cikin harin.
A halin da ake ciki dai, Isra'ila da kuma Hamas wanda su ka share kwanaki takwas su na ɗauki ba daɗi sun share kwana na farko ba tare da wani tashin hankali ba, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wutar da shugaban Masar Muhammad Mursi ya jagoranta wanda kuma ɓangarorin biyu su ka amince da ita.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu