1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaron da jirgin kasa ya markade ya mutu

Abdul-raheem Hassan
July 30, 2019

Hukumomin tsaro kasar Jamus na tsare da maharin tashar jirgin kasa tare da yin bincike kan dalilin tunkude yaron da jirgi ya markade a birnin Frankfurt.

Deutschland 40-Jähriger stößt in Frankfurt Mutter und Kind vor Zug - Achtjähriger stirbt
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Rumpenhorst

Jami'an 'yan sandan kasar Jamus sun kama mutumin da ya tunkude yaro mai shekaru takwas a kan layin dogo a babbar tashar jiragen kasa da ke birnin Frankfurt, an kuma tabbatar da mutuwar yaron. Mahaifiyarshi da maharin ya so halakata ita ma, tana kwance a gadon asibiti. Wannan lamarin dai ya girgiza jami'an tsaron Jamus, inda tuni ministan cikin gida Horst Seehofer, ya yanke hutun da yake yi, ya dawo gida don ganawa da jami'an tsaro a kan lamarin.