An kama wani ƙusa na ƙungiyar Al-Qaida
March 8, 2013Talla
Ana tuhumar Abou Ghaith ɗin ne da laifin kai hari a cikin watan Satumba na shekara ta 2001 a Amurkan wanda a ciki kusan mutane dubu ukku suka mutu.
Mataimakiyar ministan tsaro na Amurka Lisa Monaco ta ce kamun na ɗan ta'addar na da cike da mahimmanci a kokowar da suke yi ta yaƙi da ta'addanci a duniya. Ko da shi ke hukumomin Amurka basu bayyana yadda aka kamashi ba. Amma wata jaridar a ƙasar Turkiya ta ce an kama shi ne a ƙarshen watan Janeru a birnin Ankara, kana aka tusa ƙeyarsa zuwa ƙasar Jordan kafin da ga can a kai shi Amurka.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar.