An kama wani da hadin baki a harin Berlin
December 28, 2016Talla
Masu gabatar da kara na Jamus sun ce sun kama wani dan Tunisiya wanda ake kyautata tsammanin da shi aka kai harin kasuwar KIrsimeti a Berlin a makon da ya wuce. Masu gabatar da karar na tarayya suka ce mutumin mai shekaru 40 an kama shi ne bayan da aka gudanar da bincike a gidansa da kuma wurin kasuwancinsa. Sun kara da cewa an sami lambarsa a wayar Anis Amri wanda ake kyautata zaton shine ya tuka babbar motar da aka kai harin da ita a ranar 19 ga watan Disamba.