1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama wasu jiga-jigan 'yan adawa a Kamaru

October 25, 2025

Kama 'yan jam'iyyar Tchiroma Bakary da ya yi ikrarin lashe zaben Kamaru, na zuwa ne gabanin sanar da sakamakon zaben.

Ana dakon sakamakon zabe a Kamaru
Ana dakon sakamakon zabe a KamaruHoto: Etienne Mainimo/IMAGO

An kama wasu jiga-jigan 'yan adawa biyu a birnin Douala na kasar Kamaru. Hakan na zuwa ne yayin ake dakon samun sakamakon zaben kasar a ranar Litinin. 'Yan adawan da aka kama na zama manyan mambobi a jam'iyyar hamayya da ke goyon bayan dan takara Tchiroma Bakary da ya yi ikrarin lashe zaben na ranar 12 ga watan Octoba.

Karin bayani: Tababa kan sakamakon zaben Kamaru da ake jira 

Jam'iyyar MANIDEM ta ce jami'an tsaro sun yi awon gaba da ma'ajinta da kuma wasu mambobin jam'iyyar. Magoya bayan 'yan takara na bangaren adawa na ta yin gargadi kan murde sakamakon zaben.

Yayin da Tchiroma ya ke ta ikrarin ya lashe zaben, jam'iyyar Paul Biya ta zarge shi da kokarin tada zaune tsaye a kasar. A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Tchiroma ya yi gargadin cewa, duk wani yunkuri na kamashi tamkar cin zarafi ne ga al'ummar Kamaru, inda ya bukaci gwamnati ta tabbatar da nasarar da yake ikariri.