Dakile yunkurin kai hari a Jamus
June 2, 2016Talla
Wadannan mutane dai ana zarginsu da shirya kai wani hari a birnin Duesseldorf na kasar. Masu shigar da karar sun kara da cewa tuni mutum na hudu da ya bayyana shirin kai harin a birnin Paris, ya shiga hannun jami'an tsaro a kasar Faransa. Wata sanarwa da ofishin mai shigar da kara na gwamnatin tarayyar ya fitar, ta ce an cafke mutanen ne a jihohi uku na Jamus a ranar Alhamis biyu ga wannan wata na Yuni da muke ciki, inda ya ce maharan sun tsara cewa mutane biyu za su kai harin kunar bakin wake a tsakiyar birnin na Duesseldorf, kana da ga bisani wani maharin kuma ya bude wuta da bindigogi da kuma abubuwa masu fashewa domin su hallaka mutane da dama.